Isa ga babban shafi
Duniya

Kofi Annan ya nemi kasashe masu arziki su tallafa wa nahiyar Africa

Tsohon Sakateren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan ya bukaci gungun kasashe Takwas masu karfin tattalin arzikin duniya da ake kira G8 su tallafawa kasashen Afrika ta hanyar gaggauta samar da wasu sabbin matakan dakile yaduwar cin hanci da rashawa da kuma haraji da ke rarake arzikin Nahiyar. A wani rahoto da aka wallafa a yau Juma’a, Kwamitin Kofi Anan na mutane 10 da aka kafa domin duba hanyoyin ci gaban Afrika, tsohon sakataren na Majalisar Dinkin Duniyar, ya yi kira ga kasashen G8 su dinga aiwatar da gaskiya, wajen gudanar da ayyukan masana’antunsu da yadda suke tatso arzikin kasashen Afrika da ke neman yin kafada da kasashen Asiya da kuma Latin Amurka, wajen habakar tattalin arziki.Annan ya kuma bukaci kasashen na G8 su samar da sabbin dokoki ga kamfanoninsu da kuma haraji, tare da danganta matsalar cin hanci da rashawa, da ta zama ruwan dare a gwamnatocin kasashen Afrika.Rahoton yace akwai wasu kamfanoni da ke bin ta bayan fage domin kaucewa biyan  haraji domin samun ribar kasuwacin su, a yayin da Miliyoyan al’ummar Afrika ke cikin matsanancin halin karancin Abinci da tabarbarewa kiwon lafiya da kuma ilimi.Gungun kasashe G8 dai sun hada da Canada da Faransa da Jamus da Italy da Japan da Rasha da Ingila da kuma Amurka. 

Tsohon Sakkatare Janar na MDD, Kofi Annan
Tsohon Sakkatare Janar na MDD, Kofi Annan REUTERS/Allison Joyce
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.