Isa ga babban shafi
Masar

Ministocin Morsi guda hudu sun yi murabus

Wata majiya daga fadar gwamnatin Masar ta tabbatar da cewa wasu Ministocin gwamnatin Shugaba Morsi guda hudu sun yi murabus, da suka hada da na Ministan Muhalli da sadarwa sakamakon matsin lamba daga masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Jam’iyyar ‘yan uwa Musulmi ta Brotherhood.  

Ginin Hedikwatar Jam'iyyar Brotherhood ta shugaba Muhammaed Morsi na Masar da masu zanga-zanga suka abka wa kuma an samu masu kwasar ganima suka kwashe kayan ginin.
Ginin Hedikwatar Jam'iyyar Brotherhood ta shugaba Muhammaed Morsi na Masar da masu zanga-zanga suka abka wa kuma an samu masu kwasar ganima suka kwashe kayan ginin. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Majiyar tace dukkanin Ministocin sun mika takardar yin murabus dinsu zuwa ga Firaministan kasar Hisham Qandil.

Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun abka wa hedikwatar Jam’iyyar Brotherhood ta shugaba Morsi bayan wata arangama da suka yi da magoya bayan shugaban.

Kamfanin Dillacin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa an cinna wa ginin wuta da ke yankin Mogattan a birnin Al Kahira tare da jefo kayayyaki ta windo.

Shugabannin gudanar da zanga-zangar dai sun ba Shugaba Morsi wa’adi zuwa gobe Talata ya yi murabus, tare da gargadin kaddamar da zanga-zanga mai zafi da ci gaba da adawa da gwamnatinsa.

A sanarwar da babbar kungiyar ‘Yan adawar ta yada a shafin Intanet, kungiyar Tamarod ta bukaci a gaggauta gudanar da sabon zabe idan har shugaban ya yi murabus ba a wa’adin da suka ba shi na karfe 5:00 na yamma a ranar 2 ga watan Juli.

Tuni dai shugaba Morsi ya nemi a zauna teburin sasantawa amma kungiyar Tamarod ta yi watsi da kiran shugaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.