Isa ga babban shafi
Masar

Jami’an tsaro sun haramtawa Morsi fita Masar

Jami’an tsaron Masar sun kakabawa Shugaba Muhammed Morsi da manyan na hannun damarsa takunkumin tafiye tafiye akan batun ‘Yan gidan yarin da suka tsere a shekarar 2011. Amma mai ba shugaban shawara a fannin tsaro Essam al-Haddad yace wannan kamar juyin mulki ne.

Daruruwan magoya bayan Shugaba Morsi na Masar da ke Fuskantar matsin lamba daga 'Yan adawa da ke neman lalle sai ya yi murabus.
Daruruwan magoya bayan Shugaba Morsi na Masar da ke Fuskantar matsin lamba daga 'Yan adawa da ke neman lalle sai ya yi murabus. REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Jami’an tashar jirgi a Masar sun tabbatar wa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa karbar umurnin haramtawa Morsi da shugaban Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi Badie da mataimakinsa Khairat al-Shater fita daga kasar.

A shafinsa na Facebook, mai bai wa Shugaba Morsi shawara a fannin tsaro Essam al-Haddad yace wannan kamar juyin mulki ne Sojoji ke yunkurin yi.

Wannan dai na zuwa ne bayan Shugaba Morsi yace zai kafa gwamnatin hadin guiwa domin kawo karshen rikicin kasar.

Akwai dai zanga-zanga da dubban mutane Masar ke ci gaba da gudanarwa daga bangaren masu adawa da kuma masu goyon bayan shugaba Morsi.

Babban muradin ‘Yan adawa shi ne shugaba Morsi ya yi murabus. kuma ‘Yan adawa sun mamaye dandalin Tahrir inda suke ci gaba da arangama da jami’an tsaro.

Yanzu haka dai wa’adin da Sojoji suka ba bangarorin Siyasar kasar ya kawo karshe, bayan Miliyoyan ‘Yan adawa da magoya bayan Morsi sun fito suna zanga-zangar karo da juna.

Mutane akalla kimanin 50 ne aka ruwaito sun mutu, a sabon rikicin da ya barke a Masar wanda shi ne mafi muni tun juyin juya halin da mutanen kasar suka gudanar da ya kawo karshen mulki shekaru sama da 30 na Hosni Mubarak.

Rahotanni sun ce babban hafsan Sojin kasar ya gana da Shugaban ‘Yan adawa Mohamed ElBaradei, da shugaban mabiya Katolika Patriarch Tawadros na biyu da Sheikh Ahmed al-Tayeb, babban malamin Al-Azhar da kuma shugabannin mabiya sunni.

Mohammed Morsi shi ne Shugaban Demokuradiya na Farko a Masar bayan kawo karshen gwamnatin Mubarak.

Rikicin Masar dai ya shafi tattalin arzikin duniya, inda masana suke fargabar yana iya shafar farashin danyen Mai.

Ido dai ya koma ga Sojojin kasar inda ake jiran aji matakin da suka dauka bayan wa’adin da suka ba Morsi ya cika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.