Isa ga babban shafi
Masar

Sojojin Masar sun shiga tattaunawa kafin wa’adin da suka ba Morsi ya cika

Manyan hafsoshin Sojin kasar Masar sun shiga wata tattaunawar gaggawa domin daukar mataki ga rikicin siyasar kasar bayan Shugaba Morsi ya yi watsi da wa’adin da suka ba shi domin sasantawa da bangarorin siyasa wadanda ke ci gaba da Zanga-zangar adawa da gwamnatin shi.

Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Morsi na Masar.
Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Morsi na Masar. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Rahotanni sun ce Sojojin za su tattauna da shugaban ‘Yan adawa Mohamed ElBaradei, da Shugaba Mohammed Morsi da shugaban ‘Yan Sunni da shugaban mabiya Kirista da kuma wakilan jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta Brotherhood.

Wata majiya kusa da Sojin kasar ta tabbatar wa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa na AFP cewar tuni Sojin suka shiga tattaunawa domin daukar mataki akan makomar Masar. Kuma ana sa ran Sojin za su fitar da sanarwa game da matakin da suka dauka kafin wa’adin da suka ba Morsi ya cika.

Amma Shugaba Morsi ya ce babu wanda zai sa shi ya sauka daga kujerarsa, kuma a shirye ya ke ya bada ransa don kare amanar da 'yan kasar suka ba shi.

Yayin da ya ke jawabi ga al’ummar kasar, shugaba Morsi ya bukaci rundunar sojin kasar da ta janye wa’adin da ta ba shi.

A lokacin da ya ke mayar da Martani, Shugaba  Morsi  ya ce shi ne halattaccen shugaban kasa, kuma zai yi duk abinda ya dace domin kare kujerarsa.

"Na amince da 'yancin 'yan kasa na gudanar da zanga zanga, amma kuma mutunta dokokin kasa ya zama wajibi" in Shugaba Morsi, kuma ya kara da cewa idan aka samu  tashin hankali, daukar mataki a wajen sa ya zama tilas.

Morsi ya danganta tashin hankalin da sauran jami’an Gwamnatin shugaba Hosni Mubarak, inda ya bukaci masu zanga zangar da su mutunta dokokin kasa.

Shugaban ya bukaci kafa wani kwamitin sasanta 'Yan kasa da kuma kula da harkokin 'Yan Jaridu,yana mai cewa a shirye ya ke ya gana da kungiyoyi da 'Yan adawa don magance halin da ake ciki a Masar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.