Isa ga babban shafi
Masar

Sojin Masar sun ba Morsi da ‘Yan adawa wa’adin sa’o’i 48

Rundunar sojin kasar Masar ta shata wa gwamnatin Musulunci ta shugaba Morsi da ‘Yan adawa wa’adin sa’o’I 48 su gaggauta sasantawa ko kuma su dauki mataki akan rikicin siyasar kasar da ake ganin zai iya haifar da yakin basasa.

Dafifin Jama'a da ke zanga-zangar adawa da gwamnatin Morsi na Masar
Dafifin Jama'a da ke zanga-zangar adawa da gwamnatin Morsi na Masar REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

A jawabin na Sojojin a kafar Talabijin din Masar, sun ce Kasar tana cikin rudani bayan Miliyoyan ‘Yan kasar sun fito saman tituna domin adawa da gwamnatin Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi ta shugaba Morsi.

“Idan ba a cim ma bukatun Jama’a ba a wa’adin da muka diba, za mu dauki mataki” a cewar Babban hafsan Sojan Masar Janar Abdel Fattah al-Sisi.

Tuni dai ‘Yan adawa suka ba Shugaba Mrosi wa’adin sa’ao’I 24 da ya yi murabus. Kuma ikirarin na Sojin kasar ya kara farantawa ‘Yan adawar rai. Amma magoya bayan shugaba Morsi suna ganin kamar Sojin kasar suna kokarin yin juyin mulki ne saboda sun linka yawan ‘Yan adawan.

Muhammed Morsi shi ne shugaban demokuradiya na farko da aka zaba a kasar Masar bayan juyin juya halin da ya yi sanadiyar kawo karshen mulkin shekaru sama da 30 na Hosni Mubarak.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.