Isa ga babban shafi
Masar

Kasashen Duniya sun la’anci kisan magoya bayan Morsi a Masar

Kasashen duniya sun yi Allah waddai da harin da aka kai wa magoya bayan jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta hambararren shugaban kasa Mohammed Morsi wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 42 da raunata wasu daruruwan mutane.

Daruruwan mutane ne suka jikkata a harin da aka kai wa magoya bayan Morsi a ranar Litinin.
Daruruwan mutane ne suka jikkata a harin da aka kai wa magoya bayan Morsi a ranar Litinin. REUTERS/Suhaib Salem
Talla

IRAN

Gwamnatin Iran tace juyin Mulkin ya sabawa Demokradiya kamar yadda kakakin Ma’aikatar harakokin wajen kasar Abbas Araqchi ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a Masar.

Mista Araqchi ya yi zargin akwai hannun kasashen waje a cikin rikicin siyasar Masar ba tare da bayyana sunan kasar da ya ke zargi ba.

Gwamnatin Iran ta yi watsi da juyin Mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatin Demokradiyya ta Mohammed Morsi.

HAMAS

Gwamnatin Gaza ta Hamas ta yi Allah waddai da kisan magoya bayan Morsi wadanda ke gudanar da zanga-zangar adawa da juyin mulkin da Sojoji suka yi wa shugaban.

A wata Sanarwa, gwamnatin Hamas a Gaza ta yi kiran kawo karshen zubar da jini tsakanin al’ummar Masar.

KUNGIYAR TURAI

Kungiyar kasashen Turai tace tana nazarin tallafin da ta ke ba Masar bayan kungiyar ta yi Allah waddai da kisan masu zanga-zanga.

Jami’an kiwon lafiya sun ce kimanain mutane 42 ne suka mutu wasu daruruwa ne kuma suka samu rauni bayan wani hari da aka kai wa magoya bayan Morsi da asubahin Lititinin.

Kungiyar Tarayyar Turai ta La’anci harin ba tare da janye tallafin da kungiyar ke ba kasar Masar ba.

Kungiyar ta bukaci bangarorin siyasar kasar su sasanta kamar yadda sanarwar ta fito daga bakin kakakin Catherine Ashton.

Rashin janye tallafin Turai shi ne ya nuna kungiyar tana goyon bayan juyin mulkin da Sojoji suka yi wa Mohammed Morsi, kodayake kungiyar tace tana nazari akai.

Tuni dai kungiyar kasashen Turai ta kulla yarejejeniya da gwamnatin Morsi na bashin kudi euro Biliyan biyar.

Amma a bara, kungiyar tace tallafin da ta bayar na Biliyoyan kudi bayan hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak bai yi amfani ba wajen yaki da cin hanci da kare hakkin bil’adama da aiwatar da shugabanci na gari.

JAMUS

Gwamnatin Jamus ta bukaci a gaggauta gudanar da binciken wadanda ke da alhakin kai harin da aka kai wa Magoya bayan Morsi, tare da gargadin rikicin Siyasar Masar na iya haifar da yakin basasa.

QATAR

Gwamnatin Qatar mai arzikin Gas kuma kasar da ke goyon bayan jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi ta yi Allah Waddai da kisan magoya bayan Morsi 42 tare da kira ga al’ummar Masar su kauracewa duk wani abu da zai haifar tashin hankali.

SUDAN

A kasar Sudan dubban 'Yan kasar ne suka kewaye harabar ofishin jekadancin Masar a birnin Khartoum domin nuna goyon bayansu ga Mohammed Morsi da Sojoji suka tumbuke daga madafan iko a Masar.

HARIN MASAR

Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta yi zargin Jami’an tsaro ne suka kai wa magoya bayanta hari.

Amma a wata sanarwa, Sojin kasar sun ce ‘Yan ta’adda ne suka kai harin da ya yi sanadiyar mutuwar Jami’in tsaro guda.

Yanzu haka, Shugaban rikon kwarya Adly Mansour ya bayar da umurnin gudanar da binciken harin da aka kai wa magoya bayan hambararren shugaba Mohammed Morsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.