Isa ga babban shafi
Najeriya-Sudan-ICC

Najeriya ta ki mika al Bashir na Sudan ga Kotun ICC

Gwamnatin Najeriya ta kare kanta na karbar bakuncin shugaban Sudan Omar al-Bashir wanda ya kawo ziyara Abuja domin halartar taron kasashen Afrika bayan hukumar kare hakkin Bil’adama ta Human Rights Watch ta bukaci a haramtawa shugaban shiga Najeriya saboda tuhumar aikata laifukan yaki da kotun ICC ke masa.

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir a fadar gwamnatin Najeriya
Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir a fadar gwamnatin Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A ranar Lahadi ne shugaba Al Bashir ya sauka Abuja a taron shugabannin kasashen Afrika da za su yi nazarin ci gaban da aka samu wajen yaki da cutar kanjamau da cizon sauro da tarin fuka.

Kungiyoyin fararen hula sun bukaci a hana shugaba Omar Hassan al Bashir halartar taron na kwanaki biyu da aka bude a ranar Litinin, saboda sammacin kotun hukunta manyan laifuka ta ICC.

A lokacin da ya ke mayar da martani, Reuben Abati, Kakakin gwamnatin Goodluck Jonathan ya shaidawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa taron kasashen Afrika ne ya kawo Al Bashir ba Najeriya ce ta gayyaci shugaban ba.

“Najeriya ba ta da ‘Yancin tantance shugabannin da za su halarci taron kasashen Afrika” inji Abati

Tun a 2009 da 2010 ne kotun hukunta laifukan yaki ta bayar da sammaci kamo al Bashir akan rikicin yankin Darfur wanda Majalisar Dinkin Duniya tace rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 300,000.

Najeriya dai Mamba ce a kotun ICC kuma tana da ‘Yancin cafke al Bashir. Amma wasu kasashen Afrika da dama suna zargin kotun ta damu ne da shugabannin kasashen Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.