Isa ga babban shafi
Najeriya

An yi musayar wuta a Gamborungala a Najeriya

Rahotanni a Najeriya sun ce an yi musayar wuta da hare haren bama bamai a garin Gamborungala a Jahar borno da ke kan iyaka da kasar Kamaru bayan an kafa dokar hana fita a garin Potiskum. Majiyar Soji da mazauna garin sun ce tun a daren Litinin ne rikicin ya barke har zuwa wayewar safiyar Talata amma babu wani cikakken bayani da ya fito daga Jami’an tsaro.

Garin Maiduguri kamar an yi ruwa an dauke wanda ke karkashin dokar ta-baci
Garin Maiduguri kamar an yi ruwa an dauke wanda ke karkashin dokar ta-baci Reuters/Afolabi Sotunde
Talla

Yanzu haka kuma an kafa dokar hana fita a garin Potiskum a Jahar yobe inda Sojoji ke shiga gida gida domin farautar ‘Yan bindiga.

Babu dai wani bayani daga Jami’an tsaron akan dalilin da ya sa suka kafa dokar hana fita a dai dai lokacin da al’ummar musulmi ke shirin gudanar da bukin Salla bayan kammala azumin watan Ramadan.

Wani Mazauni Garin Gamboringala yace lamarin ya faru ne bayan da aka harbi wani mutum da ya nemi ya gujewa jami’an shige da fice kuma tun a lokacin ne suke jin karar harbin bindiga.

Wannan kuma na zuwa ne bayan mutuwar wasu mutane akalla 35 a biranen Bama da Malam Fatori sakamakon wata musayar wuta tsakanin Jami’an tsaro da ‘Yan bindiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.