Isa ga babban shafi
Masar

Magoya bayan Morsi sun bejirewa Gwamnati

Magoya bayan hambararren shugaban kasar Masar Mohammad Morsi sun ci gaba da gudanar da zanga-zangar inda suke jaddada bukatarsu ta ganin an sake dawo da shi a kan karagar mulkin kasar. Wannan kuwa duk da irin kashedin da hukumomin kasar suka yi na ko dai a dakatar da zanga-zangar ko kuma a yi amfani da karfin domin kawo karshensu.

Daruruwan Mata da ke zanga-zangar nuna goyon bayansu ga hambararren shugaban kasar Masar Mohammed Morsi
Daruruwan Mata da ke zanga-zangar nuna goyon bayansu ga hambararren shugaban kasar Masar Mohammed Morsi REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Jami’ar Al-Azhar da ke birnin Alkahira, ta yi tayin shiga tsakani domin warware wannan rikici na siyasa da ake fama da shi a kasar Masar.

Tsawon mako biyu ke nan Gwamnatin Masar ke yin barazanar watse sansanin ‘Yan Uwa musulmi wadanda ke gudanar da zanga-zanga tun lokacin da Sojoji suka hambarar da gwamnatin Morsi a ranar 3 ga watan Yuli.

A gobe Talata Magoya bayan Morsi sun yi kiran gudanar da gagarumar Zanga-zanga bayan kammala hutun Sallar Azumi.

Amma gwamnatin rikon kwarya ta Adly Mansur ta sha alwashin watse sansanin masu zanga-zangar a Rabaa al-Adawiya da Nahda.

Babban Malamin Jami’ar al Azhar Ahmed al-Tayyeb ya kaddamar da wani kudiri na shiga tsakanin rikicin kasar domin hada bangarorin biyu don a cim ma sulhu.

Zuwa yanzu dai kimanin Mutane 250 ne aka ruwaito sun mutu tun lokacin da Sojoji suka yi wa Morsi juyin Mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.