Tsohon Shugaban Najeriya, kuma jigo a sabuwar Jam’iyar APC, Janar Muhammadu Buhari, ya yi bayani game da sabuwar Jam’iyyarsu da za ta fafata da PDP a zaben 2015 inda yace sun dunkule ne domin gyara Demokuradiya a kasar. Kuma Buhari ya yi bayani game da tsayawa takarar shi a zaben da ke karatowa tare da mayar da Martani ga PDP Mai Mulki a tattaunawarsu da Bashir Ibrahim Idris.
Sauran kashi-kashi
-
Abdulaziz Abdulaziz kan cikar Tinubu shekara guda a karagar mulkin Najeriya
A jiya ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya cika shekara guda a karagar mulki, kuma RFI Hausa ta samu tattaunawa da mai bashi shawara akan harkokin yada labarai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, a kan batutuwa da dama da suka kunshi tattalin arziki, noma, tsaro, darajar naira da kuma kuncin rayuwa. Ga kadan daga cikin tattaunawar da suka yi da Bashir Ibrahim Idris.30/05/202403:28 -
Farfesa Abba Gambo kan gargaɗin manoma a game da shuƙin wuri a damunar bana
Rahoton wanda National Bureau of Statistic ta fitar a makon da ya gabata, ya cewa an fuskacin hauhawan farashin kayayyaki da sama da kashi 33 da rabi cikin 100 a watan Afrilun da ya gabata.22/05/202403:32 -
Prof. Tukur Abdulkadir kan zargin Firaministan Isra'ila da aikata laifukan yaki
Kotun Duniya ICC ta zargi Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ministan tsaron sa tare da shugabannin Hamas da aikata laifuffukan yaki.Wannan mataki ya haifar da cece kuce sakamakon irin asarar rayuka da ake ci gaba da yi a Gaza da Gabar yamma da kogin Jordan da kuma Rafah. Dangane da tasirin matsayin kotun da kuma abinda zai yi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Tukur Abdulkadir na Jami'ar Jihar Kaduna.Ku latsa alamar sauti domin jin yadda zantawar su ta gudana...21/05/202403:26 -
Hon Sama'ila Muhammad a kan dokar kare hakkin Yara a Najeriya
'Yan Najeriya na ci gaba da tafka mahawara a kan dakatar da auran wasu marayu 100 da ministar kula da harkokin matan kasar ta bukata a Jihar Neja, saboda abinda ta kira sabawa dokar kare hakkokin yara.Yanzu haka kungiyoyi daban daban sun ruga kotu domin kalubalantar ministar.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da lauya kuma tsohon 'dan majalisar tarayya, Hon Samaila Muhammed, wanda yace dokar da ake magana a kai ta sabawa dokokin kasa.Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren hirar.20/05/202403:34 -
Attahiru Bafarawa kan shirin ƴan adawa na tinkarar jam'iyya mai mulki a 2027
A Najeriya, yanzu haka wasu daga cikin manyan ‘yan adawar ƙasar cikin su harda wadanda suka tsaya takarar zaɓen shekarar 2023 sun fara tintibar juna domin tsara yadda za su tinkari jam’iyya mai mulki a zaɓe mai zuwa. Rahotanni sun ce akwai yiwuwar kafa wata sabuwar jam’iyya domin kalubalantar gwamnati mai ci.Dangane da wannan yunkuri, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa. Kuna iya latsa alamar sauto domin sauraren hirar.15/05/202403:18