Isa ga babban shafi
Sudan

Sudan ta tsawaita wa’adin da ta ba Sudan ta Kudu

Kasar Sudan ta tsawaita wa’adin da ta dibar wa Sudan ta kudu na dakile magudanar danyen man fetur da ke ratsawa zuwa kasar Sudan ta kudu, har zuwa ranar shida ga watan Satumba sakamakon shiga tsakani da kungiyar kasashen Afrika ta yi.

Shugaban kasar Sudan Omar al-bashir
Shugaban kasar Sudan Omar al-bashir
Talla

A kasar Sudan ne danyen man kasar Sudan ta kudu ke bi zuwa kasuwannin kasashen duniya, a watan jiya ne kasar ta tsayar da ranar Bakwai ga wannan wata da muke ciki za ta hana bi da man inda take zargin Sudan ta kudu da marawa ‘Yan tawayen da ke ja da Gwamnatin Shugaba Omar Bashir baya.

Kasar Sudan ta kudu tace sam babu gaskiya a cikin zargin da ake yi mata.

Kungiyar kasashen Afrika ta shiga cikin zancen domin hana samun gibi wajen fitar da danyen man da kasar Sudan ta kudu ke yi, inda ita kuma kasar Habasha ta ke yin nata kokarin domin yin sulhu.

Kasar Sudan ta kudu wadda ta sami ‘yancin kanta daga Sudan a shekara ta 2011, na dogaro ne kacokan kan man fetur da Allah ya hore mata, kuma dakile hanyar fitar da man zuwa ga kasashen Turawa da wasu kasashen na iya durkusar da kasar.

Ita kanta Sudan za ta cutu idan har ta hana domin ana biyanta wasu kudade na bi cikin kasar da danyen mai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.