Isa ga babban shafi
Masar

Kasashen Duniya sun la’anci al’amarin da ke faruwa a Masar

Shugabannin Kasashen duniya sun bayyana bacin ransu da yadda hukumomin sojin kasar suka abkawa magoya bayan hambararen shugaban kasa, Mohamed Morsi, abinda ya haddasa rasa rayuka da dama. Ma’aikatar lafiyar kasar tace mutane 278 aka kashe, cikin su har da ‘Yan Sanda kusan 50, yayin da Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi tace an kashe mutane sama da 2,000.

Sojoi suna aikin watse sansanin magoya bayan Morsi inda aka samu hasaran rayukan mutane da dama
Sojoi suna aikin watse sansanin magoya bayan Morsi inda aka samu hasaran rayukan mutane da dama REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Kasashen Iran da Qatar da Birtaniya da Turkiya sun yi Allah Waddai da yadda aka yi amfani da karfi wajen murkushe magoya bayan Mohammed Morsi wadanda suka kwashe kwanaki suna zanga-zangar neman a dawo da shi saman madafan iko bayan Sojoji sun hambarar da gwamnatin Shi.

Wakilin Kamfanin Dillacin Labaran Faransa yace akalla mutane 124 ne suka mutu a ranar Laraba bayan da ‘Yan sanda suka abka cikin sansanin da magoya bayan Morsi ke gudanar da zanga-zanga a birnin Al Kahira.

Wakilin na AFP yace ya kirga gawawwakin mutanen a Masallacin Rabaa al Adawiya kuma yawanci sun mutu ne da harsashen bindiga.

Gwamnatin Iran ta danganta al’amarin a matsayin kisan Kiyashi, tare da yin Allah Waddai da al’amarin.

Ma’akatar harakokin wajen Iran tace idan ba’a dauki matakan sulhu ba, Masar na iya fadawa yakin basasa.

An kwashe tsawon shekaru Iran na adawa da Masar amma sai a lokacin Morsi ne kasashen biyu suka amince da yarjejeniyar inganta huldarsu. Kuma a zamanin Morsi ne shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad, ya kai ziyara kasar Masar a karon farko tsawon shekaru 30.

A nata bangaren, Gwamnatin Qatar da ke nuna goyon bayan gwamnatin ‘Yan uwa Musulmi ta yi Allah Waddai da yadda aka yi amfani karfi wajen murkushe magoya bayan Morsi a birnin al Kahira.

Gwamnatin Qatar ta la’anci al’amarin wanda ta danganta a matsayin kisan bayin Allah, kamar yadda Kamfanin dillancin labaran kasar na QNA ya ruwaito sanarwar daga ma’aikatar harakokin wajen kasar.

Gwamnatin Qatar da yi kira ga Mahukuntan Masar su kawo karshen yin amfani da karfin Soji akan masu zanga-zanga, tana mai gargadin hakan zai iya raba hankalin ‘yan kasar a shekaru masu zuwa.

Gwamnatin Birtaniya ta bukaci mahukuntan kasar Masar su dakatar da matakin yin amfani da karfii, bayan ta yi Allah waddai da al’amarin.

Sakataren harakokin wajen Birtaniya William Hague yace suna masu yin nadama da hasarar rayukan mutanen da aka samu a kasar Masar.

Gwamnatin Turkiya tace yin amfani da karfin Soji kan masu zanga-zanga abu ne da kasashen Duniya ba za su amince da shi ba, tana mai danganta yadda aka murkushe magoya bayan Morsi a matsayin kisan kiyashi.

Ofishin Firaminista Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga kasashen Duniya su gaggauta shiga tsakanin rikicin masar domin yin shiru ba zai haifar wa kasar abu mai kyau ba.

A ranar 3 ga watan Yuli ne Sojoji suka hambarar da gwamnatin Morsi, kuma tun a lokacin ne magoya bayan shi suka kaddamar da zanga-zangar neman a dawo da shi  saman madafan iko wanda shi ne shugaban Dimokuradiya na farko a kasar.

Gwamnatin Jamus da kungiyar Tarayyar Turai sun yi kira ga bangarorin Masar su gaggauta komawa teburin sasantawa don gudun kada rikicin ya koma irin na Syria.

‘Yan sandan kasar dai sun yi amfani ne da hayaki mai sa hawaye a sansanin magoya bayan Morsi bayan sun kewaye Masallacin Rabaa al-Adawiya da kuma Dandalin Al Nahda a birnin al Kahira.

Duk da wannan matakin na murkushe masu zanga-zanga amma Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi ta bukaci magoya bayanta su fito domin nuna takaici da la’antar gwamnatin kasar.

Kakakin Kungiyar Brotherhood Gehad al-Haddad yace akalla mutane 250 ne aka kashe, wasu kuma kimanin 5,000 ne suka jikkata. Kuma Ma’aikatar cikin gidan Masar tace Jami’an tsaro guda biyu ne aka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.