Isa ga babban shafi
Masar

Sama da mutane 500 ne suka mutu a rikicin Masar

A kasar Masar an wayi gari cikin dokar ta-baci da aka kafa bayan artabun da aka yi tsakanin Jami’an tsaro da magoya bayan Morsi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 464. Sojin kasar sun kafa dokar ta-baci ta tsawon wata guda ne a yankunan kasar 13.

Jami'an tsaro suna harba hayaki mai sa hawaye a dandalin magoya bayan Morsi domin watse su a Rabaa Adawiya a birnin al kahira
Jami'an tsaro suna harba hayaki mai sa hawaye a dandalin magoya bayan Morsi domin watse su a Rabaa Adawiya a birnin al kahira REUTERS/Asmaa Waguih
Talla

Ma’aikatar Lafiya tace kimanin mutane 421 ne suka mutu, a sakamakon rikicin a sassan yankunan kasar, kuma akwai Jami’an tsaro 43 da suka mutu.

Arangamar da aka yi a ranar Laraba tsakanin Jami’an tsaro da magoya bayan Morsi, shi ne labarin da ya mamaye jaridun Masar da na kasashen Yankin Gabas ta tsakiya.

Akwai hare hare da Jaridun kasar suka ruwaito an kai wa Mujami’un kiristoci tare da zargin magoya bayan Morsi ne suka kai harin domin mayar da martani.

Rikicin na Masar tsakanin gwamnati da magoya bayan Morsi shi ne rikici mafi muni da aka samu a kasar tun bayan zanga-zangar da ta yi sanadin kawo karshen mulkin Hosni Mubarak.

Jam’iyyar ‘Yan uwa muslmi tace kimanin mutane 2,200 ne suka mutu, sama da 10,000 ne kuma suka samu rauni.

Wannan ne ya sa Mataimakin shugaban kasa Mohamed ElBaradei ya yi murabus, yana mai cewa ya girgiza da hasarar rayukan da aka samu a kasar.

‘Yan sanda dai sun abka sansanin magoya bayan Morsi ne guda biyu inda suka kwashe kwanaki suna zanga-zangar neman a dawo da shi saman madafan iko bayan Sojoji sun tumbuke shi a ranar 3 ga watan Yuli.

Manyan kasashen Turai da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya da Iran da Qatar da Turkiya dukkaninsu sun yi Allah Waddai da yadda aka yi amfani da karfi wajen murkushe magoya bayan Morsi.

Amma Firaministan kasar Hazem al-Beblawi ya yaba da yadda Jami’an tsaron suka watse gangamin magoya bayan Morsi, tare da ikirarin gwamnati a shirye ta ke ta aiwatar da tsarin da Sojoji suka samar da zai cim ma gudanar da zabe a 2014.

Jam’iyyar ‘Yan uwa msulmi tace wannan kisan kiyashi ne aka yi wa magoya bayanta tare da kiran gudanar da wani sabon gangami domin la’antar gwamnati.

Rikicin na Masar ya bazu zuwa yankunan Alexandria da Beheira da Suez da Ismailiya da kuma Assiut da Menya.

Yanzu haka kuma Shugaban Faransa ya kira jekadan Masar zuwa fadarsa a birnin Paris domin tattauna hanyoyin magance rikicin kasar. Yayin da kuma Firaministan kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bukaci kwamitin Sulhu na Majalisar Duniya ya gudanar da taron gaggawa game da rikicin Masar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.