Isa ga babban shafi
Guinea

Babban hafsan sojan kasar Guinea Bissau ya ce ba zai bar mulki ba

Babban hafsan sojojin kasar Guinea Bissau, Janar Antonio Injai, ya ce ba ya da niyyar yin marabus daga mukaminsa kamar yadda wasun ‘yan siyasar kasar ke bukata, lamarin da ya kara jefa jama’ar kasar a cikin shakku dangane da yiyuwar kafa gwamnatin farar hula kafin zaben ‘yan majalisar dokoki kasar, da aka tsara gudanarwa a cikin watan satumba mai zuwa. Guinea Bissau dai kasa ce da ta yi kaurin suna ta fanni juyin mulkin soja a yankin yammacin Afirka, kuma babban kwamandan askarawan kasar ya furta wannan kalami ne a lokacin taron, kan batutuwan da suka shafi tsaron kasar a birnin Bissau. 

Hafsan sojan Guinea Bissau, Janar Antonio Indjai
Hafsan sojan Guinea Bissau, Janar Antonio Indjai
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.