Keita na Mali ya kai ziyara Chadi
Zababben shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita na gudanar da ziyarar aiki ta farko a wata kasa ta waje inda ya ziyarci kasar Chadi tare da ganawa da shugaban kasar Idris Deby a wani gari da ke gabashin kasar. Ibrahim Boubakar Keita wanda ake shirin rantsarwa a ranar 4 ga watan satumba, ya ce ya je kasar Chadi ne domin bayyana godiyarsa dangane da irin rawar da ta taka wajen ‘yantar da Mali daga hannun ‘yan tawaye da suka kwace yankin Arewaci.
Wallafawa ranar:
Kasar Chadi ce ta fi kowace kasa yawan asarar sojoji a yakin Mali, wadanda ked a kwarewar yaki a sahara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu