Isa ga babban shafi
Masar

Za’a kammala rubuta kundin tsarin mulkin Masar a Nuwamba

Hukumomin Kasar Masar sun ce za’a kammala rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar, dan maye gurbin na hambararen shugaban kasa, Mohammed Morsi a karshen watan Nuwamba. Kwamitin da ke rubuta sabon kundin ya bayyana cewar, za’a gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a don amincewa da kundin, makwanni biyu bayan kammala rubuta shi. Yanzu haka mutane 60 ke can suna aikin rubuta kundin.

Shugaban rikon kwarya na kasar Masar Adly Mansour
Shugaban rikon kwarya na kasar Masar Adly Mansour REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.