Isa ga babban shafi
DRC Congo

MDD ta fara amfani da jirgi mara matuki a rikicin Congo

A karo na farko tawagar samar da zaman lafiya ta Mjalisar Dinkin Duniya a jiya Talata ta kaddamar da soma aiki da Jirgin leken asirin da baya dauke da matuki, a yankin gabashin kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo.

Jirgin MDD mara matuki a Congo
Jirgin MDD mara matuki a Congo AFP
Talla

Wannan kuma na zuwa ne da zummar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin da ya share tsawon shekaru ana zubar da jini a cikinsa, haka kuma kasa da wata guda bayan kawo karshen kungiyar yan tawayen M23 a yankin

Jirgin leken asirin dan madaidaici da aka kera a kasar Italiya a jiya Talata ya yi tashinsa na farko daga filin sauka da tashin jirage na birnin Goma babban birnin yankin Arewacin Kivu a gabashin kasar ta Congo, a lokacin da ake gabatar da shi ga manema labarai a gaban shugaban tawagar samar da zaman lafiya ta Mjalisar Dinkin Duniya Herve Ladsous.

A cewar Ladous jirgin mai saukar angulu nauyi ne da shi, kuma bashi da hanzari da kuma hayaniya,

“Wannan na’ura ce, da bata da nauyi ga hanzari ga kuma sirri, a yanzu zamu iya gani da ido daga saman yankunan da ake da matsaloli irin na tsaro, ina tsammanin za a samu canji mai yawa.” Inji Ladous.

Ya kara da cewa yanzu rundunar Majalisar Dinkin Duniya ta Munisco na da issasun dakarun shiga tsakani, kuma za ta samu idanu na ganin wasu kungiyoyin mayakan da suke ta da kayar baya a yankin, ganin yanzu an kawo karshen kungiyar yan tawayen M23.

A tsokacin da ya yi ma sashen Hausa na gidan radiyo Faransa, Dr. Ja'afar Lawal Dabai, Malami a jami'ar Kampala dake Kampala a Uganda, ya ce Majalisar Dinkin Duniyan ta yi hakan ne saboda ta kakkabe sauran kungiyoyin 'yan tawaye da suka rage a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.