Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

An fara samun kwanciyar hankali a Bangui

Hankula sun dan soma kwantawa a birnin Bangui fadar gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, bayan da aka share tsawon kwanaki ana tashe-tashen hankula da kuma kai hare hare a kan musulmi da ake dangantawa da kawancen kungiyoyin ‘Yan tawayen Seleka da ke kan karagar mulkin kasar.

Al'ummar Musulmi suna salla a Bangui kasar Jamhuriyar tsakiyar Afrika
Al'ummar Musulmi suna salla a Bangui kasar Jamhuriyar tsakiyar Afrika AFP PHOTO/FRED DUFOUR
Talla

A tsawon yinin jiya Laraba, sojojin Faransa da aka tura zuwa kasar, sun ci gaba da aikin karbe makamai daga hannun ‘Yan tawayen na Seleka da kuma sauran mayakan sa-kai, yayin da jama’a suka ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da an samu tashin hankula ba. Sai dai wasu majiyoyi na cewa har yanzu jama’a na a cikin fargaba musamman ma a wasu unguwanni na birnin da jami’an tsaro ba sa iya shiga.

Shugabannin Addini a kasar sun yi kiran a sasantawa tsakanin Musulmi da Kirista game da rikicin day a lakume rayukan daruruwa mutane.

Mayaka daga bangaren Musulmi da Kirista ne suke bi gida gida suna kashe fararen hula tare da kone gidajen mutane da motoci.

Imam Oumar Kobine Layama shugaban mabiya Addinin Islama a Jamhuriyyar tsakiyar Afrika ya yi kiran samun zaman lafiya a lokacin da yak e jagorantar bayar da tallafin abinci ga dubban mutanen da suka shiga mawiyacin hali.

Baya ga kokarin kwance damarar mayakan tsohuwar kungiyar ‘yan tawayen Saleka, dakarun sojan Faransa ne, ke da alhakin hana faruwar duk wata ramuwar gayya da mabiya addinin Kirista zasu iya kai wa fararen hula musulmi, domin huce takaicinsu kan yadda tsoffin mayakan kungiyar ‘yan tawayen da akasarinsu musulmi ne suka kwace mulkin kasar a watan maris na wannan 2013 wadanda suka gallazawa kiristoci.

Wannan dai ya haifar da tura dakarun shiga tsakani na kasar Faransa a farkon makon da ya gabata a kasar da ta kasance tsohuwar kasar da Faransar ta yi wa mulkin mallaka, wadanda zasu ci gaba da zama kasar kafin rundunar dakarun Nahiyar afrika ta karbe su.

A lokacin da ya ziyarci kasar a ranar talatar da ta gabata, kwana guda bayan kashe dakarun Faransa biyu, shugaban kasar Faransa François Hollande ya bayyana cewa an tura dakarun na faransa ne, domin ceton rayukan al’umma fararen hula a kasar da ba shugabanci ba ma’aikatu balantana hukumomin da zasu tabbatar da tsaron rayukan jama’a.

Rikicin baya bayan nan da ya barke a kasar ta Jamhuriyar Tsakiyar Afrika ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 400, kamar yadda kungiyar bayar da agaji ta Croix rouge ta sanar inda tace mafi yawancinsu kuma an kashe su ne a birnin Bangui babban birnin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.