Isa ga babban shafi
Masar

Ana tuhumar Morsi da aikata manyan laifuka a Masar

Masu gabatar da kara a kasar Masar sun ce Hambararren shugaban kasa Mohammed Morsi zai gurfana a gaban kotu tare da wasu mambobin kungiyar Hamas da Hezbollah akan wani hari da aka kai wa Gidan yari inda aka kashe Jami’an tsaro a lokacin zanga-zangar kin jinin gwamnatin Mubarak a 2011.

Wasu magoya bayan hambararren shugaban Masar Mohamed Morsi, suna zanga-zanga a kasar Masar
Wasu magoya bayan hambararren shugaban Masar Mohamed Morsi, suna zanga-zanga a kasar Masar REUTERS/Suhaib Salem
Talla

Akwai mambobin kungiyar Hamas ta Falesdinawa da Hezbollah ta Lebenon kusan 70 da za’a yanke wa hukunci ba a idonsu ba.

Masu gabatar da kara sun zargi Morsi na Brotherhood da Kungiyoyin Hamas da Hezbollah da wasu mayakan jihadi akan sun jagoranci wani hari da aka kai wa gidan yari da ofishin ‘Yan sanda a farkon lokacin da aka fara zanga-zangar da ta yi awon gaba da Hosni Mubarak, inda suka yi ikirarin an kashe ‘Yan sanda tare da taimakawa dubban ‘Yan gidan yari suka tsere.

Masu gabatar da karar sun ce mambobin Brotherhood da Hamas da Hezbollah sun kai harin ne a gidan yari domin taimakawa 'Yan uwansu su tsere.

Wata majiya tace cikin wadanda suka tsere daga gidan yarin sun hada da shugaban Brotherhood Wadi al-Natrun da shehin malamin kasar Qatar Yousef al-Qaradawi.

Yanzu haka an kaddamar da bincike akan Morsi game da ballewar ‘yan gidan yarin a ranar 28 ga watan Janairun 2011. Kuma tuni ake zargin tsohon shugaban akan ya bayar da umurnin a kashe masu zanga-zanga a zamanin mulkin shi na shekara daya.

Akwai kuma zargi da masu gabatar da kara suka shigar a gaban kotu akan Morsi ya ci amanar kasa saboda kawancensa da Hamas.

Mohammed Morsi shi ne shugaban demokuradiya na farko da aka zaba a kasar Masar amma a watan Yuli ne Sojoji suka hambarar da gwamnatin shi bayan wata zanga-zangar kin jinin shi da ‘yan adawa suka gudanar.

Tun lokacin da aka hambarar da Morsi, an kashe mutanen Masar sama da 1,000 sakamakon arangama tsakanin magoya bayan Morsi da ‘Yan sanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.