Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Sojin kasashen Burundi da Chadi sun yi musayar Wuta a jamhuriyar Afruka ta tsakiya

Sojin da aka aika domin tabbatar da tsaro a kasar Jamhuriyar Afruka ta tsakiya, sun yi musayar Wuta a tsakanin su, a birnin Bangui na kasar

Soji a Jamhuriyar Afruka ta tsakiya
Soji a Jamhuriyar Afruka ta tsakiya REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Wani babban Kwamandan Yaki daga bangaren Rundunar Sojin kasar Burundi Kanal Pontien Hakizimana, ya shaidawa Kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa AFP cewar Sojinsa, na kokarin kwace Makaman tsofaffin ‘yan tawaye ne, kawai sai Dakarun kasar Chadi suka jefa masu Gurnet, tare da buda masu Wuta babu kafkaftawa.

Wannan ne yasa a cewar sa, Sojin kasar Chadi suka maida martani ta hanyar buda Wuta, abinda yayi sanadin jikkatar akalla Sojin kasra Chadi 3.

Babban Kwamandan Sojin da kuma bangaren Sojin kasar Faransa dai na zargin Dakarun Sojin kasra Chadi da goyon bayan ‘yan tawayen Seleka da ya kamata a kwace wa Makamai.

Hakizimana ya ce daga bisani Sojin kasar Chadi sun sake dawowa da yawa suka kuma afkawa Dakarun Sojin na Burundi.

Dangantaka tsakanin Burundi da Chadi dai ta fara sami ne, tun bayan da aka fara aike da Dakarun samar da zaman lafiya a kasar Jamhuryar Afruka ta tsakiya.

Baya ga Dakaru 850 da ta aika a Jamhuriyar Afruka ta tsakiya dai kasar Burundi, na da akalla Dakaru 5,500 da ke aikin samar da zaman lafiya a Somaliya, a yayin da ta yi aniyar aike da dakarunta a kasar Mali.

Al’amurra a jamhuriyar Afruka ta tsakiya dai na ci gaba da rincabewa, a yayin da a kwanannan ma an zargi Sojin kasar Faransa da nuna banbanci tsakanin bangarorin ‘yan tawayen 2 da ake fada da su a kasar masu banbancin Addini da Kabila.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.