Isa ga babban shafi
Masar

An sake kai harin bam na uku a Cairo

Wani harin bom da aka kai a kasar Masar ya raunata wasu sojojin kasar guda hudu yayin da rikicin siyasar kasar ke ci gaba da kamari. Wannan shi ne karo na uku da ake kai hare hare cikin mako guda, tun bayan da hukumomin kasar suka bayyana kungiyar ‘yan uwa Musulmi a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

Wasu mutane tare da Jami'an tsaron sun tsaya inda aka kai harin bam a birnin al Kahira na Masar wanda ya raunata Sojoji guda hudu
Wasu mutane tare da Jami'an tsaron sun tsaya inda aka kai harin bam a birnin al Kahira na Masar wanda ya raunata Sojoji guda hudu Reuters
Talla

An kai harin ne ofishin jami’an tsaron kasar a yankin Sharqiyya kuma ya lalata wani bagaren ginin, wanda shi ne hari na uku da aka kai a kasar cikin mako guda.

Rundunar sojin kasar Masar ce ta tabbatar da kai harin yayin da hukumomin kasar ke shirin gudanar shirin jin ra’ayoyin mutane game da sabon kundin tsarin mulkin kasar, wanda shi ne matakin farko na komawar kasar kan turbar dimokuradiyya bayan Sojoji sun hambarar da gwamnatin Morsi shugaban dimokuradiya na farko.

A ranar Talata akalla mutane 15 suka rasa rayukansu bayan harin da wani dan kunar bakin wake ya kai a yankin Mansoura, wanda shi ne hari mafi muni tun bayan hamabarar da gwamnatin Mohammed Morsi.

Hukumomin kasar sun daura alhakin wadannan hare hare kan kungiyar ‘Yan uwa musulmi yayin da kungiyar ke ci gaba da nisanta kanta ga duk wasu hare hare da aka kai ko kuma za a kai anan gaba.

Sanya sunan kungiyar cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda da gwamanatin rikon kwaryar Masar ta yi a makon da ya gabata, yanzu haka na nufin daruruwan ‘yan kungiyar da ake tsare da su za su fuskanci fushin hukuma, cikin har da wasu daliban jami’o’I da aka kama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.