Isa ga babban shafi
Rwanda

Ana bikin cika shekaru 20 da kazamin rikicin kasar Rwanda

Kasar Rwanda ta fara bukukuwan cika Shekaru 20 da kazamin zub da jinin da aka yi a kasar a Shekarar 1994 a tsakanin ‘Yan kabilar Hutu da Tutsi a yayin da ake shirin gudanar da jerin Gwano na musamman a sauran sassan kasar.

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagamé
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagamé REUTERS/Noor Khamis
Talla

Jami’an Gwamnati da kuma wasu mutanen da suka tsira a wannan tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar Dubban Daruruwan mutane a sassan kasar sun hadu a Dandalin tunawa da tashin hankalin a Kigali, inda aka tayar da Belar wutar a gaban Ministan harkokin wajen kasar ta Rwanda Louise Mushikiwabo.

An dai yi taron ne ana daf da fara jerin Gwanon da za’a gudanar a Garuruwa da Kauyukan kasar da ke a yankin tsakiyar Afrika.

A ranar bakwai ga Watan Afrilu ne za’a fara zaman makoki na tunawa da rasa rayukan mutane da aka yi a wannan lokaci.

A lokacin tashin hankali dai an bayyana adadin mutanen da suka mutu da suka kai Dubu dari takwas daga bangaren ‘yan kabilar Tutsi ‘yan tsiraru.

An ce Sojin sa-kai na Hutu masu rinjaye ne suka gudanar da kisan a Shekarar 1994.

Babban abin tashin hankali shi ne yadda ‘yan Hutu suka kai wa wata Makarantar ‘yan Mata ta Nyange hari. Dai bayan dai aka rika tsame dalibai ‘yan kabilar Tutsi ana bindigewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.