Isa ga babban shafi
DRC Congo

Gwamnatin Congo ta yi wa Ƴan tawayen M23 afuwa

Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo Joseph Kabila, ya sanya hannu a kan dokar da ke yi wa Ƴan tawayen ƙungiyar M23 afuwa waɗanda suka aikata laifufuka daban daban a ƙasar. Majalisar Ɗinkin Duniya ta yaba da wannan mataki.

Shugaban Jamhuriyyar Congo Joseph  Kabila, a ziyarar da ya kai wa 'Yan tawayen M23 à Kiwanja
Shugaban Jamhuriyyar Congo Joseph Kabila, a ziyarar da ya kai wa 'Yan tawayen M23 à Kiwanja RFI/Léa-Lisa Westerhoff
Talla

Sai dai Afuwa ba ta shafi aikata laifukan yaƙi ba da suka haɗa da ayyukan ta’addanci da fyaɗe da gallazawa mutane ba.

Ƴan tawayen sun amince ba zasu goyi bayan sauran Ƴan tawayen da ke yaƙi a ƙasashen da ke maƙwabtaka da Congo ba a ƙarƙashin yarjejeniyar da gwamnatin ta ƙulla da su.

Gwamnatin Congo da Majalisar Ɗinkin Duniya sun daɗe suna zargin Gwamnatocin Rwanda da Uganda akan suna taimakawa Ƴan tawayen M23 tun soma rikicin ƙasar a watan Afrilun 2012.

Gwamnatin Congo dai ta buɗe kofa ne ga Ƴan tawayen M23 da suka tsere zuwa Uganda su dawo gida bayan kawo ƙarshen yaƙin ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.