Isa ga babban shafi
Masar

An zabi Ibrahim Mahlab a matsayin Firimiyan Masar

Ministan gidaje ne Ibrahim Mahlab aka zaba sabon Firaministan kasar Masar wanda ke da alhakin gudanar da zaben shugaban kasa bayan gwamnatin Beblawi ta yi murabus.A jiya Litinin ne gwamnatin Hazem al-Beblawi ta yi murabus a wani mataki na bazata kafin a gudanar da zaben shugaban kasa da ake hasashen Babban Hafsan Sojan kasar Abdel Fattah al-Sisi zai tsaya takara.

Ibrahim Mahlab, Sabon Firaministan Masar
Ibrahim Mahlab, Sabon Firaministan Masar REUTERS/Stringer/Files
Talla

Ibrahim Mahlab, Tsohon Jam’in gwamnatin Mubarak ne, kuma a cikin jawabinsa bayan zabensa Firaminista ya sha alwashin yaki da ta’addanci a Masar tare da yin kokarin kafa gwamnati.

A watan Yuli ne aka kafa gwamnatin Beblawi bayan Sojoji sun tumbuke Mohammed Morsi, shugaban dimokuradiya na farko a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.