Isa ga babban shafi
Masar

Rasha ta bayyana goyon baya ga takarar Sisi a Masar

Yau Alhamis Shugaban kasar Rasah Vladimir Putin ya bayyana goyon bayan shi ga takarar da babban hafsan Sojan Masar Field Marshal Abdel Fattah al-Sisi zai yi.Mr Putin ya bayyana haka ne, yayin ziyarar da Field Marsha Sisi ya kai birnin Moscow a yau Alhamis. Shugaba Vladimir Putin yace dangantaka tsakanin kasashen Masar da Rasha za ta kara danko bayan zaben kasar da za a yi, a wani lokaci cikin wannan shekarar.Mr Putin yace shi, dama sauran al’ummar kasar Rasha suna wa Sisi fatan alheri a yunkurin shi na takarar shugabancin kasar.Takarar ta Sisi, mai shekaru 59 a duniya, na samun goyon bayan wasu ‘yan kasar ta Masar da ma jami’an tsaron da ke fatan ganin kasar ta sami shugaban da zai tunkarin tashe tashen hankulan siyasar da kasar ke fuskanta.Rasha na kokarin amfani da dusashewar da dantakatakar Masar da Amurka ke yi, bayan da hukumomin Washigton suka janye wasu daga cikin tallafin da take baiwa alkahira, bayan da Sisi ya hambarar da zababbiyar gwamnati Mohamed Mursi na kungiyar ‘yan uwa Musulmi.A watan Nuwamban bara Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha Sergei Lavrov da tsaro Sergei Shoigu suka kai ziyara a birnin Alkahira, inda suka nemi farfado da dangantaka tsakanin kasashen 2, da ta dakushe tun zamanin taraiyyar Suviet. 

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.