Isa ga babban shafi
Masar

Kotun Masar ta zartar da hukuncin kisa akan mutane 26

Kotun kasar Masar ta zartar da hukuncin kisa akan wasu mutane 26 da aka samu da aikata laifukan ta’addanci da suka kunshi yunkurin kai wa wani jirgin ruwa hari a gabar ruwan Port Said.

Jiragen ruwaa gabar ruwan Port Said.
Jiragen ruwaa gabar ruwan Port Said. REUTERS/Stringer
Talla

Kotun ta kuma zargi mutanen da samar da Bama bamai wadanda aka yanke wa hukunci ba a gaban idonsu ba, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka ruwaito.

Wannan hukuncin dai na zuwa a dai dai lokacin da sabon Firaministan kasar Ibrahim Mahlab tsohon Jami'in gwamnatin Hosni Mubarak ya sha alwashin yaki da ta’addanci a kasar Masar.

Kasar Masar dai ta shiga rudani musamman bayan da Sojoji suka hambarar da gwamnatin Morsi, almarin da ya haifar da kazamar zanga-zanga da hare haren ‘Yan ta’adda.

Tun lokacin dai sama da mutane 1,000 ne aka ruwaito sun mutu, wasu da dama ne kuma Jami’an tsaro suka cafke, yawancinsu magoya bayan Mohammed Morsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.