Isa ga babban shafi
Rwanda-Afrika ta Kudu

Rwanda da Afrika ta kudu suna takun saka

Dangantaka tsakanin Kasar Rwanda da Afrika ta kudu na ci gaba da tabarbarewa bayan dukkanin kasashen sun kori Jami’an diflomasiyarsu akan wani yunkuri na kisan Janar din Sojan kasar Rwanda a birnin Johannesburg wanda ya nemi mafaka a Afrika ta kudu.

Janar din sojan Rwanda Faustin Kayumba Nyamwasa da ya tsere zuwa kasar Afrika ta kudu
Janar din sojan Rwanda Faustin Kayumba Nyamwasa da ya tsere zuwa kasar Afrika ta kudu AFP/MARCO LONGARI
Talla

Afrika ta kudu dai tana zargin, akwai sa hannun Jami’an diflomasiyar Rwanda wajen yunkurin kashe Faustin Kayumba Nyamwasa, wanda tsohon jagoran rundunar Sojan Rwanda ne.

‘Yan adawar kasar Rwanda sun ce wasu gungun ‘yan bindiga ne suka kai wa Janar din Sojan hari a gidansa da ke Johannesburg a ranar Litinin din makon jiya.

A lokacin da ya ke mayar da martani, Kannedy Gihana na Jam’iyyar adawa ta Rwanda National Congress RNC, yace gwamnatin Rwanda ta dade tana amfani da ofishin jekadancinta a matsayin wata cibiyar da suka fi mayar da hankali ga ayyukansu.

Mr Kennedy yace zasu ji dadi idan har kasar Afrika ta kudu zata dauki mataki zuwa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin duniya, a cewarsa wannan da ya saba dokokin duniya, domin ba wannan ne karon farko ba tun a 2010 aka aika da Sojoji a Afrika ta kudu.

‘Yan adawar kuma sun ce suna fatar a rufe ofishin jekadancin Rwanda har abada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.