Isa ga babban shafi
Masar

Kotun Masar ta yanke wa mutane 526 hukuncin kisa

Kotun kasar Masar ta yanke hukuncin kisa, kan magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammad Morsi su 529, da aka samu da laifin shiga zanga-zangar da gwamnatin kasar ta haramta gudanarwa a bara.

Hambararren shugaban Masar Mohammed Morsi tare da wasu manyan shugabannin 'Yan uwa Musulmi a kotu
Hambararren shugaban Masar Mohammed Morsi tare da wasu manyan shugabannin 'Yan uwa Musulmi a kotu REUTERS
Talla

Wannan ne karon farko da kotun ke yanke hukuncin kisa akan mutane masu tarin yawa a lokaci daya, tun bayan da sojoji suka kifar da Morsi na jam’iyyar ‘yan uwa Musulmi, daga madafun iko a watan Yulin bara.

Wasu daga cikin laifukan da kotun da kama mutanen, sun hada da kisan ‘Yan sanda da hare hare kan mutane da gine ginen gwamnati.

Mutanen da aka yanke wa hukuncin suna cikin magoya bayan kungiyar ‘Yan uwa Musulmi 1,200 da ke fuskantar shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.