Kotun Masar ta dakatar da shari’ar Morsi
Kotun kasar Masar ta dakatar da Shari’ar da ake yi wa Mohammed Morsi bayan Lauyan da ke kare tsohon shugaban da ake tuhuma da laifin bayar da umurnin kisan masu zanga-zanga ya nemi a canza alkali.
Wallafawa ranar:
Morsi shugaban mulkin dimokuradiya na farko a Masar yana fuskantar shari’a ne tun lokacin da aka tumbuke shi daga madafan ikon Masar akan zargin ya bayar da umurnin kisan masu zanga-zangar kin jinin shi a watan Disemba na 2012.
Lauyan da ke kare tsohon shugaban ya bukaci a canza biyu daga cikin Alkalan da ke Shira’ar, yana mai zargin daya daga cikinsu ya tattauna da ‘Yan jarida game da Shari’ar.
Babu tabbas dai ko Kotun kasar zata amince da bukatar Lauyan, kodayake ana saran Kotun kolin zata yanke hukunci a ranar 9 ga watan Afrilu.
Akwai zarge-zarge da dama ake tuhumar Mohammed Morsi da suka hada da batun ballewar ‘Yan gidan yari a lokacin zanga-zangar adawa da gwamnatin Hosni Mubarak a 2011.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu