Isa ga babban shafi
Masar

Masar: Sisi ba zai yi watsi da kiran mutane ba

Babban hafsan Sojin kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi yace ba zai yi watsi da kiran mutanen Masar akan bukatar ya tsaya takarar shugaban kasa ba, a zaben kasar da za’a gudanar a watan Afrilu wanda ake ganin babu tantama shi zai lashe zaben.

Magoya bayan Janar Abdel Fattah al-Sisi a wani gangamin goyon baya a dandalin Tahrir a birnin al Kahira
Magoya bayan Janar Abdel Fattah al-Sisi a wani gangamin goyon baya a dandalin Tahrir a birnin al Kahira Reuters/路透社
Talla

Magoya bayan Sisi suna ganin babu wanda zai iya magance matsalolin kasar da ke cikin rudani tsawon shekaru uku da aka kaddamar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin Hosni Mubarak.

Janar Sisi ya kasance mai karfin fada a ji a cikin Masar tun lokacin da ya tumbuke Mohammed Morsi, shugaban dimokuradiya na farko a kasar.

Kafin tsayawa takarar shugaban kasa, sai Sisi ya tube kakin Soja tare da sauka daga mukaminsa na Ministan tsaro.

Kamfanin Dillacin Labaran MENA ya ruwaito Marshal Sisi yana cewa ba zai yi watsi da bukatar mutanen Masar ba idan suna bukatar ya tsaya takarar shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.