Isa ga babban shafi
Guinea Bissau

Kumba Yala,tsohon shugaban Guinea Bissau ya rasu.

Tsohon shugaban kasar Guinea Bissau, Kumba Yala ya rasu yau juma’a  yana dan shekaru 61 da haihuwa a duniya.Wani na hanu damar sa ya sheidawa manema labarai da cewa ya rasu ne sanadiyar bugun zuciya. 

(Photo : Marie-Laure Josselin /RFI)
Talla

Kumba Yala ya mulki kasar ta Guinea Bissau ce daga shekarar 2000 zuwa 2003 inda sojin kasar suka yi masa juyin mulki.

Gabanin mutuwar tsohon Shugaban kasar, iyalansa sun garzaya da shi zuwa wani asibiti sojin garin Bissau mai suna Bra.

Gwamantin ta bakin ministan yada labarai na kasar Guinea Bissau, Fernando Vaz, za a gudanar da zaman makoki na kwanaki uku a duk ilahirin kasar, wata hanyar girmama marigayi Kumba Yala.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.