Firaministan Libya ya yi murabus
Firaministan Libya Abdallah al-Thani ya yi murabus a ranar Lahadi, bayan an kai masa hari da iyalansa, kuma matakin na zuwa ne kafin ya kafa sabuwar gwamnati bayan Majalisa ta tube Ali Zeidan da aka zarga da gazawa wajen samar da cikakken tsaro a kasar.
Wallafawa ranar:
A cikin sanarwar, al Thani yace ba zai amince da mukamin Firaministan ba saboda barazana ga rayuwar shi.
Thani wanda Ministan tsaro ne, a ranar Talatar makon jiya ne aka zabe a matsayin Firaministan bayan majalisa ta tube Ali Zeidan.
A ranar Assabar ne ‘Yan bindiga suka kai wa Firaministan hari a garin Tripoli kan hanya, amma rahotanni sun ce harin bai haifar da wani ta’adi ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu