Guinea Bissau
Sai an shiga zagaye na biyu a zaben Guinea Bissau
Hukumar Zabe a kasar Guinea Bissau tace za’a gudanar da zaben shugaban kasar zagaye na biyu saboda rashin samun wanda ya samu rinjayen lashe zaben kai tsaye. Sakamakon da hukumar ta bayar ya nuna cewar, Jose Mario Vaz na Jam’iyar African Party shi ne akan gaba da kashi sama da 40 na kuri’un da aka kada, yayin da Nuno Gomez Nabiam ke bi masa kashi sama da 25.
Wallafawa ranar:
Talla
Hukumar zaben tace za’a gudanar da zaben ne a ranar 18 ga watan Mayu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu