Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Dattijan Najeriya ta amince a tsawaita dokar ta baci

‘Yan Majalisar Dattijan Najeriya sun amince a tsawaita dokar ta baci a Jahohin Borno da Yobe da Adamawa da ke yankin arewa maso gabacin kasar kamar yadda Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bukata. Tuni ‘Yan Majalisar Wakilai suka amince a tsawaita dokar, duk da wasu mutanen kasar suna sukar matakin saboda kazancewar hare haren Mayakan Boko Haram.

Wasu Mata da yara da suka fake a ofishin 'Yan sanda a garin Maiduguri da ke cikin dokar ta baci
Wasu Mata da yara da suka fake a ofishin 'Yan sanda a garin Maiduguri da ke cikin dokar ta baci (Photo : AFP)
Talla

Karo na biyu ke nan ana tsawaita dokar ta bacin a yankunan bayan kafa dokar, yanzu tsawon shekara guda.

Sanata Abdulkadir Alkali Jajere daya daga cikin ‘Yan Majalisar da ke wakiltar jihar Yobe, ya shaida wa RFI Hausa cewa ba da ra’ayinsu ba ne a tsawaita dokar illa kawai majalisa ce ta fi karfinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.