Kotun Masar ta yanke wa magoya bayan Morsi 54 hukunci
Wata kotu a kasar Masar ta yankewa wasu magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi su 54 hukuncin daurin rai rai a gidan yari. An yankewa mutanen wannan hukuncin ne, bayan da kotun ta same su da laifukan yin mu’amulla da kungiyoyin ‘yan ta’adda da aikata kisan kai da kuma tayar da tarzoma.
Wallafawa ranar:
Akwai kuma wasu mutane 104 da Kotun ta yanke wa hukuncin dauri tsakanin shekara daya zuwa 10 kuma cikinsu har da wasu mata daliban Makaranta guda uku.
Tun bayan hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi na Jam’iyyar ‘Yan Uwa musulmi ake yankewa magoya bayanta hukunci tare da haramta ayyukan Jam’iyyar a Masar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu