Isa ga babban shafi
Masar

Kasashen Duniya sun yi tir da hukuncin kisa akan 'Yan uwa musulmi

Gwamnatin Iran ta yi gargadin cewa hukuncin kisa da aka yanke wa mutane kusan 700 a Masar, mataki ne da zai kara hura wutar rikicin kasar, musamman sabbin hare haren ta'addanci akan Jami'an tsaro. Tuni Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suka yi tir da hukuncin da aka yanke wa magoya bayan hambararren shugaban kasa Mohammed Morsi.

Hambararren shugaban Masar Mohammed Morsi tare da wasu manyan shugabannin 'Yan uwa Musulmi kargame
Hambararren shugaban Masar Mohammed Morsi tare da wasu manyan shugabannin 'Yan uwa Musulmi kargame REUTERS
Talla

A ranar Litinin ne, Alkalin Kotun da ya yanke wa daruruwan magoya bayan hambararren shugaban kasa Mohammed Morsi hukuncin kisa ya sake gabatar da wani hukuncin kan Shugaban Jam’iyyar ‘Yan Uwa musulmi Mohammed Badie da wasu mutane 682.

Kotun ta kama Badie ne da sauran magoya bayan Morsi da laifin kisa da yunkurin kisan ‘Yan sanda a kudancin Minya a ranar 14 ga watan Agusta, ranar da ‘Yan sanda suka kashe daruruwan magoya bayan ‘Yan uwa Musulmi a birnin al Kahira.

Tun lokacin da Sojoji suka hambarar da gwamnatin Morsi a watan Yulin bara, ake ci gaba da tarwatsa ayyukan Jam’iyyar ‘Yan uwa Masulmi a Masar.

Hukuncin akan daruruwan mutane ya janyo suka daga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin Bil’adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.