Ana tattauna matsalar tsaron Najeriya a Afirka ta Kudu
Shugabannin kasashen Afirka da ke halartar bikin rantsar da Jacob Zuma domin ci gaba da shugabancin kasar Afrika ta Kudu, a yau asabar suna gudanar da wani taro na musamman kan matsalar tsaro da ta dabaibaye Najeriya.
Wallafawa ranar:
Kakakin gwamnatin Afirka ta Kudu Clayson Monyela, ya ce akwai shugabannin kasashen fiye da 20 da ke halartar bukukuwan rantsar da Zuma, kuma ko shakka babu za su halarci wannan taro domin duba yadda za a taimaka wa Najeriya fita daga cikin matsalar tsaron da take fama da ita.
A lokacin da ya shiga zauren da ake rantsar da Zuma, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, an tarbe shi ne ta taken Bring Back Our Girls, wato a dawo da ‘yan matan Chibok da aka sace.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu