Isa ga babban shafi
Masar

Zaben Shugaban kasa a Masar

Al’ummar kasar Masar sun fara jefa kuri’ar zaben shugaban kasa, inda ake hasashen Tsohon babban hafsan Sojan kasar shi zai lashe zaben wanda ya hambarar da gwamnatin ‘Yan uwa Musulmi ta Mohammed Morsi. Wannan shi ne zaben shugaban kasa karo na biyu da aka gudanar a Masar cikin shekaru biyu.

Al'ummar kasar Masar suna layin jefa kuri'ar zaben Shugaban kasa a birnin al Kahira a ranar 26 ga watan Mayu 2014
Al'ummar kasar Masar suna layin jefa kuri'ar zaben Shugaban kasa a birnin al Kahira a ranar 26 ga watan Mayu 2014 REUTERS/Asmaa Waguih
Talla

Abdulfatah al-Sisi wanda ya hambarar da Morsi a watan Yuli, yana takara ne tsakanin shi da Hamdeen Sabbahi.

Magoya bayan Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi sun kauracewa zaben wadanda aka haramta ayyukansu a kasar.

Akwai kuma wasu gungun kungiyoyin matasa da suka ce zasu kauracewa zaben saboda kyamatar Soja ya jagoranci kasar da ke fatar samun dorewar mulkin demokuradiya bayan sun yi zanga-zangar hambarar da Hosni Mubarak wanda ya kwashe shekaru sama da 30 yana mulki a kasar.

Za’a dai kwashe kwanaki biyu ana gudanar da zaben daga yau Litinin har zuwa Talata, inda za’a bayyana sakamakon zaben a ranar 5 ga watan Yuni.

A watan Yulin bara ne Abdulfatah Al–Sisi ya hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi, shugaban dimukuradiya na farko a tarihin Masar.

Yanzu haka kuma ana tsare da Morsi akan wasu tuhume tuhume da ake masa da suka shafi kisan masu zanga-zanga a zamanin shi.

Hambarar da gwamnatin Morsi dai ya janyo hasarar rayukan mutane da dama yawancinsu magoya bayan Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi, kuma akwai ‘yayan Jam’iyyar kimanin 16,000 da aka cafke.

A yakin neman zabensa al Sisi yace zai yi kokarin kawo ci gaba a kasar Masar a fannoni da suka shafi Ilimi da Noma da kuma samar da ayyukan yi.

Abokin adawarsa kuma Sabahi ya yi kira ne ga matasan kasar su ba farar hula dama sabanin Soja tare da yin alkawalin magance matsalar cin hanci a kasar.

Amma dukkanin ‘Yan takarar guda biyu, sun yi alkawalin ba za su halatta ayyukan Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.