Isa ga babban shafi
Algeria

Kwararru sun gano akwanin nadar bayanai na Air Algerie

Kwararru da ke aikin binciken sanadin faduwar jirgin Algeria a kasar Mali sun sake gano akwatin nadar bayanai na biyu daga cikin tarkacen jirgin a inda ya tarwatse. Akwai wata tawagar kwararru da zasu isa inda jirgin ya fadi a yau Assabar domin gano musabbabin faruwar hadarin jirgin wanda ya taso daga Burkina faso zai nufi kasar Algeria.

jirgi mai saukar Angulu yana isa inda jirgin Algeria ya fadi a Mali .
jirgi mai saukar Angulu yana isa inda jirgin Algeria ya fadi a Mali . Reuters/ECPAD
Talla

Jirgin wanda ya fadi a yankin kasar Mali yana dauke ne da mutane 118, kuma babu wanda ya rayu a cikinsa.

Kasar Faransa ta ware kwanaki uku domin zaman makokin wadanda suka mutu a hadarin jirgin inda mutane 54 a cikin jirgin Faransawa ne.

Sanarwar da ta fito daga fadar shugaban kasa tace Daga Ranar Litinin, za’a sassauta tutar kasar zuwa kasa har zuwa kwanaki uku na zaman makokin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.