Isa ga babban shafi
Afrika

Bakin haure 2,000 suka mutu a Teku

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla ‘Yan kasashen Afrika kusan 2,000 suka fada teku suka kuma mutu a kokarin da suke na tsallakawa Turai don samun rayuwa mai inganci a cikin wanna shekara. Wani rahotan da hukumar kula da ‘Yan gudun hijira ta rubuta yace akasarin mutuwar an same su ne a cikin watanni uku da suka gabata.

Ma'aikatan agaji suna kokarin ceto bakin Haure a Ruwan Italiya
Ma'aikatan agaji suna kokarin ceto bakin Haure a Ruwan Italiya Reuters/Marina Militare
Talla

Kakakin hukumar Melissa Fleming tace tashin hankalin da ake samu Libya ya taimakawa masu safarar mutane zuwa Turai, abinda ke da hadari sosai.

Hukumar tace mutane 124,380 suka yi nasarar tsallakawa Turai a cikin wanna shekarar daga Afrika.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.