Isa ga babban shafi
Liberia

Cutar Ebola na ci gaba da mamaye kasar Laberiya

Hukumomi a kasra Laberiya na ci gaba da kokawa akan yanda Cutar Ebola ke batun mamaye kasar, da kuma yanda mutane ke ci gaba da mutuwa

ebolaviruspictures.com
Talla

Ministan harkokin tsaron kasar Liberia Brownie Samukai ya ce yanzu haka cuytar ebola da ke yaduwa kamar wutar daji na neman share al’ummar kasar daga doran kasa.

A wani jawabi mai sosa rai da ya gabatar wa kwamitin sulhu, na Majalisar dunkin Duniya, ministan ya ce kasar na fuskantar barazanar da ta zarce ta yakin basasar da ya shafi kasar a shekarun baya, inda ya nemi taimakon kasashen Duniya domin shawo kan Annobar Cutar ta Ebola da a halin yanzu ta gagari hukumomin kasar.

A wani labarin kuma kasra Amurka da ta bayyana cewar da wuya a iya magance Cutar a Nahiyar Afruka cikin dank ankanin lokaci, ta ce za ta bada Dala miliyan 10 a matsayin agaji don biyan ma’aikatan lafiyar da ke yaki da cutar ta Ebola a Afruka ta Yamma.

Masu lura da al’amurrra dai na tsokaci kan yanda ake samun warakar masu kamuwa da Cutar a Nahiyar Turai, amma a Afruka matsalar sai dada kamari take.

Shugaban kungiyar USAID Rajiv Shah ya ce za’ayi anfani da kudin da Amurka ta yi tayin bayarwa ne wajen jigilar ma’aikatan lafiya da za su yi aiki a kasashen Laberiya, da Guinea, da Saliyo da kuma tarayyar Nigeria.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dunkin Duniya ta ce mutane 2,288 ne cutar ta kashe a wadanan kasashe.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.