Isa ga babban shafi
Masar

Kotu da daure Maza takwas akan Luwadi

Wata kotu a kasar Masar ta yanke wa wasu Maza guda takwas hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari, bisa wani hoton bidiyo da aka yada a Intanet, inda masu gabatar da kara suka ce na wani bikin auren jinsi guda ne. Kodayake babu wani sashe a dokar Masar da aka bayyana haramta yin luwadi, amma kotu ta kama su da laifin gurbata tarbiya a Masar, bayan an cafke su a watan Satumba.

Auren jinsi guda.
Auren jinsi guda. Reuters/Tobias Schwarz
Talla

Hoton bidiyon ya nuna wasu maza biyu suna sumbatar juna tare da yin musayar zobe a tsakaninsu. Mutane sun ta aika bidiyon a shafukan zumunta irinsu Facebook da Twitter da Youtube.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.