Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Shugaban Sojan Burkina ya gana da ‘Yan adawa

Shugaban rikon kwarya na Sojan Burkina Faso Isaac Zida, ya gana da shugabannin ‘Yan adawa a birnin Ouagadougou fadar gwamnatin kasar, wadanda ke jagorantar zanga-zangar da ta yi awon gaba da Blaise Compaore, shugaban da ya kwashe shekaru 27 yana shugabanci a kasar.

Isaac Zida, Shugaban sojan Burkina Faso
Isaac Zida, Shugaban sojan Burkina Faso AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Talla

Cikin wadanda suka yi ganawar da shugaban kasar na Soja, akwai shugaban masu adawa a zauren majalisar kasar. sai dai babu wani cikakken bayani dangane da abinda suka tattauna akai.

Sojoji dai sun tarwatsa gangamin daruruwan mutanen Burkina Faso da suka fito suna zanga-zangar adawa da kwace mulki da Sojojin suka yi a Ouagadougou tare da karbe ikon kafofin yada labaran kasar.

Kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ta yi kira ga ‘Yan adawar Burkina Faso da Sojojin kasar su sasanta domin tsayar da lokacin da za’a gudanar da sabon zaben shugaban kasa don samun zaman lafiya a cikin kasar.

Shugaban Ghana John Dramani Mahama ne ya yi wannan kiran wanda shi ne shugaban Kungiyar ECOWAS.

Tuni Amurka da Majalisar Dinkin Duniya Duniya da Tarayyar Afrika suka yi kira ga Sojojin kasar Burkina Faso su gaggauta mika mulki ga farar hula tare da gargadin kakabawa kasar takunkumin idan har Sojin suka bijirewa wannan kiran.

Tarayyar Turai ta yi kira ga Sojojin Burkina Faso su mutunta ‘yancin al’ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.