Majalisar Dinkin Duniya
Ana bukin ranar samar da magewayi a duniya
MAJALISAR Dinkin Duniya ta bukaci kawo karshen yadda mutanen duniya kusan biliyan daya ke bayan gida a filin Allah, matakin dake haifar da yada cututtuka masu yaduwa.Rahotan Majalisar yace kasar India ita tafi fama da wanan matsala, abinda ke tilastawa mata zuwa bayi a daji, sai kuma kasahsen Indonesia, Pakistan, Nepal da China.Majalisar tace rabin mutanen kasar Liberia a filin Allah suke zuwa bayan gida, yayin da a Saliyo kashi daya bisa uku basa gina bayan gida.Majalisar tace mutane miliyan 39 basu da bayan gida a Najeriya, Habasha, Sudan, Nijar da Mozambique.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: