Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan ya yi alkawarin gudanar da tsaftaccen zabe a 2015

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a sakonsa dangane da zagayowar ranar ta Kirismeti, ya bukaci al’ummar kasar da su yi sauran ‘yan kasar da ke cikin kunci sakamakon ayyukan ta’addanci da kasar ke fama da su.

Shugaban Tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Hakazalika Jonathan ya ce gwamantinsa za ta ci gaba da fada da wadanda ya kira masu tsatsauran ra’ayin addini, kafin daga bisani ya jaddada wa al’ummar kasar cewa gwamnatinsa za ta bai wa hukumar zabe dukkanin abinda take bukata domin ganin cewa an gudanar da zabubukan shekara mai zuwa a cikin kyakkyawan tsari.

A wani bangare na sakonsa shugaban na Najeriya ya bukaci ‘yan siyasa da su sanya kishin kasa a gaba da kuma kaucewa tunzura jama’a ko kuma yada karerayi a lokacin yakin neman zabensu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.