Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Jami’an tsaron shugaban Burkina Faso sun sauya manufa kan Isaac Zida

Sojin dake gadin fadar shugaban kasar Burkina faso, sun yi watsi da kiran da suka yi a farko, inda suka bukaci Firaiminista Isaac Zida, ya yi murabus daga mukaminsa na firaministan kasar

Le Premier ministre burkinabè Isaac Zida sur la sellette face au mécontentement de la garde présidentielle.
Le Premier ministre burkinabè Isaac Zida sur la sellette face au mécontentement de la garde présidentielle. AFP PHOTO
Talla

Janye wannann kudirin na zuwa ne bayan firaminiustan mai rikon kwarya, ya yi alkawarin ba zai wargaza zaratan sojin ba, kamar yadda wata majiyar soji a kasar ta tabbatar a jiya Alhamis.

Yawancin jami’an sojin dai, sun shaidawa kamfanin dillacin labaran faransa AFP, cewa yanzu dai firaministan ya sanar da cewa zai bar sojojin domin cigaba da gudanar da ayyukansu na tsaro a fadar shugaban kasar, ko da yake daga farko, an bukaci ya sauke su.

A cewarsa, babu wani sauran batu dangane da kawo karshen ayyukan Dakarun sai ma dai kara kaimi da zai bisa taimaka masu domin inganta ayyukan su, ta yadda ba iya fadar shugaban kasa ayyukan nasu zasu takaita ba.

A dayan bangaren kuwa, majiyar ta sojin , ta bayyana cewa, ba dakarun bane suka dora Isaac Zida akan mukamin da ya ke rike dashi na Firaministan, kana ba su da ikon dakatar da shi daga kujerarsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.