Isa ga babban shafi
Masar

Masar ta yi wa IS ruwan wuta a Libya

Kasar Masar ta kaddamar da hare haren sama kan kungiyar IS a Libya bayan Mayakan sun wallafa wani hoton bidiyo da ke nuna yadda suka kashe kiristocin Masar 21. Rundunar sojin kasar tace ta kai hare haren ne kan sansanin mayakan tare da lalata makamansu.

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi
Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi REUTERS/Egyptian Presidency/Handout via Reuters
Talla

Tuni Shugaban kasar Abdel Fattah al Sisi ya yi alkawarin daukar fansa kan mayakan a jawabin da ya yi wa al’ummar Masar ta kafar talabijin bayan ya sanar da zaman makoki na kwanaki bakwai.

A cikin watan Disemba ne Mayakan IS suka yi garkuwa da Kiristocin na Masar a garin Sirte da ke ikon Mayakan.

Amma a sakon hoton Bidiyon wanda aka wallafa a ranar Lahadi, Mayakan sun nuna yadda suka fille kan Kiristocin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.