Isa ga babban shafi
Jordan

Jordan ta yi wa IS ruwan wuta

Kasar Jordan tace cikin kwanaki uku ta tawartsa wurare 56 da ta ke tunanin mabuyar mayakan IS da suka kona matukin jirgin kasar da ransa a makon da ya gabata. Tuni dai Jordan ta sha alwashin yakar Mayakan IS, domin mayar da martani ga kisan Maaz Kassasbeh da mayakan suka kona bayan kame shi a lokacin da jirginsa ya fadi a kasar Syria a watan Disemba.

Jiragen Sojan kasar Jordan
Jiragen Sojan kasar Jordan REUTERS/Muhammad Hamed
Talla

Shugaban sojin saman kasar Manjo Janar Mansour al Jabour bai yi Karin bayani kan ta’adin da suka yi ba, sai dai ya ce hare haren da suka fara ranar alhamis sun lalata kashi 20 na mabuyar mayakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.