Isa ga babban shafi
Jordan

Jordan ta mayar da martani bayan kisan matukin Jirgi

Gwamnatin kasar Jordan ta sanar da hallaka wasu ‘yan ta’adda guda biyu da ake tsare da su, a matsayin martani ga mayakan IS da suka kona matukin jirgin kasar da ransa. Kuma Jordan ta sha alwashin kashe dukkanin ‘Yan ta’addan da ta ke tsare da su.

Safi Yousef na biyu a hannun dama, mahaifinMuath al-Kasaesbeh, Matukin Jirgi da Mayakan ISIS suka kashe
Safi Yousef na biyu a hannun dama, mahaifinMuath al-Kasaesbeh, Matukin Jirgi da Mayakan ISIS suka kashe REUTERS/Muhammad Hamed
Talla

Jordan ta kashe wata mata mai suna Sajida al-Rishawi ‘Yar asalin Iraqi da Ziad al-Karboli domin mayar da martani ga mayakan IS da suka nemi yin musaya da Rishawi a madadin matukin jirgin kasar da suka kona da ransa a wani hoton bidiyo.

Tuni dai kasar Jordan ta sha alwashin kisan duk wadanda ta tsare da su akan laifin kisa domin mayar da martani ga kisan Maaz al-Kassasbeh da mayakan IS suka kona bayan sun cafke shi a lokacin da jirginsa ya fadi a Syria a watan Disemba.

Amurka da Faransa da Birtaniya da Japan da Jamus da Majalisar Dinkin Duniya dukkaninsu sun yi allawaddai da kisan Sojan saman na Jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.