Isa ga babban shafi
Jordan

kungiyar IS ta kashe matukin Jirgi dan kasar Jordan

Rahotannin da ke fitowa daga yankin gabas ta tsakiya, na nuna cewar kungiyar nan ta IS mai ikrarin yin Jihadi, ta kashe matukin Jirgin nan dan kasar Jordan da kungiyar ta yi garkuwa da shi

RFI Hausa
Talla

A wani hoton Bidiyon da kungiyar ta fitar, ta nuna yanda ta kona matukin JIrgin dan asalin kasar Jordan da ta kama a cikin Watan Disamba da ransa.

Hoton Bidiyon da kungiyar ta fitar ya nuna wani mutum da aka bayyana shi a matsayin Maaz al-Kassasbeh na ci da Wuta, sai dai ya zuwa yanzu babu cikakken bayani kan yadda aka yi kisan da kuma bagiren da aka aiwatar da kisan.

Kungiyar ta IS dai ta sha gudanar da ire-iren wadannan kame-kamen na yin garkuwa da mutane daga bisani kuma ta kashesu, bisa kasawar wasu hukumomin kasa-da-kasa na biya masu bukatunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.